Sunday, 4 November 2018

Kwana 3 bayan hatsarin jirgin sama an samu jariri da ranshi

Kwanaki uku bayan wani jirgin saman kasar Indonesia yayi hatsari aka samu wannan yaro mahaifiyarshi ta saka shi a cikin wata jaka mai bada kariya (life jacket) a lokacin da jirgin yake shirin yin hadari domin ya kare yaron.


Kwanaki uku da yin hatsarin jirgin wanda ya hallaka illahirin fasinjoji da ke cikinsa, jami'an tsaro masu binciken gano gawarwakin mutane da hatsarin jirgin ya rutsa da su suka gano wannan yaron a cikin ruwa ba tare da wani abu ya cutar da shi ba.

Hakika duk wanda Allah Ya rayashi babu wanda ya isa ya kashe shi, kuma duk wanda Allah Ya tsareshi babu wani abu da ya isa ya cutar dashi.
Allah Ya nuna mana ayarSa a zihiri.

Allah Ka kara mana imani sannan Ka tsare mu kamar yadda Ka tsare wannan yaro.
Daga Datti Assalafiy.

No comments:

Post a Comment