Tuesday, 27 November 2018

Likitoci, malaman Jiyya, da marasa lafiya sun runtuma da gudu bayan da wani ya shiga asibiti da zazzabin Lassa

A jiya, Litinin wani mara lafiya ya isa babban asibitin Sapele a jihar Delta da cutar zazzabin Lassa, ai kuwa ana ganinshi sai Likitoci, malaman jiyya hadda ma sauran marasa lafiya suka ranta a na kare.

Ma'aikatan asibitin sun kira jami'an 'yan sanda inda suka bukaci su cire mara lafiyar daga asibitin, kamar yanda national helm ta ruwaito, saidai 'yansandan sun ki cire mara lafiyan inda suka bukaci likitocin da su dubashi.

Dadai mara lafiyan yaga ana kyamarshi dai ya bar asibitin da kanshi.

Rahotanni sun nuna cewa saida ma'aikatan asibitin suka yi feshi dan kar a samu burbushin cutar.

No comments:

Post a Comment