Wednesday, 7 November 2018

Magidanci ya bindige matarshi da dan uwanshi daya kama suna lalata har lahira

Cin amana abune me matukar bata rai da karya zuciyar wanda akawa, musamman idan cin amanar aurece ko kuma tsakanin masoya kuma ace da wanda baka tsammanine, hakane ta faru da wani magidanci inda ya kama kaninshi da matarshi turmi da tabarya.

Oleg Kirkunov dan kasar Rasha me shekaru 54 ya gayyaci dan uwanshi, Evgeny me shekaru 65 gidanshi inda suka ci abincin dare aka yi zumunci, saboda dare yayi sai dan uwan me gidan yace zai kwana kamin da safe ya wuce, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.

Tsakar dare Oleg ya irin juya dinnan sai baiga matarshi kusa dashi ba, sai ya tashi ya tafi nemanta, yana tsakar gida sai ya jiyo motsi/nishi a wani daki, ya karasa, ai kuwa sai yaga abinda bai yi tsammani ba, matarshi ce da dan uwanshi suke lalata.

Dama mafaraucine, sai kawai ya dauko bindigarshi ta farauta ya kakkabe, ya dirkawa matarshi harsashi a kai, dan uwan nashima da yaga haka sai yayi sauri ya saka kaya dan ya tsere, aikuwa shima be barshi ba, ya dirka mishi harsashi, nan duk su biyun suka fafi a mace.

Oleg na gama harbe su sai ya dauki waya ya kira 'yan sanda yace musu ga abinda ya aikata, nan aka zo aka tafi dashi.

Rahotanni sun bayyana cewa, za'a ajiyeshi nan zuwa watan Janairu kamin a gama bincike dan yanke mai hukunci.

Saidai wani abin ban mamaki da ya faru shine, mutane da dama a shafukan sadarwa na yanar gizo sun jinjinawa magidancin da wannan kisan da yawa matarshi da dan uwanshi inda suka rika kiranshi da gwarzo.

Wasu ma sunce ko da sune abinda zasu aikata kenan, basu damu da zaman gidan yari ba.

No comments:

Post a Comment