Thursday, 29 November 2018

MAGOYA BAYAN JAM'IYYAR APC SU DUBU BIYU SUN SAUYA SHEKA ZUWA PDP A JIHAR SOKOTO

Magoya bayan jam'iyyar APC sama da dubu biyu ne suka sauya sheka zuwa PDP a jihar Sokoto.


Taron ya samu halartar dan takarar Dan majalisa Tarayya Kware/Wamako Alhaji Bello Guiwa da shugaban jam'iyyar PDP na Wamakko Alhaji Ahamad Aliyu Girafshe da kuma manyan baki da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da shugabannin 'yan kasuwa.

Haka kuma shugabannin  jam’iyyar PDP na karamar hukumar Wamakko karkashin jagorancin Alhaji Nura Sahabi sun yi alkawarin marawa jam’iyyar PDP baya a zaben 2019 da za a yi a jihar Sokoto da Nijeriya baki daya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment