Thursday, 8 November 2018

MAHUKUNTAN KASAR DUBAI ZA SU TALLAFAWA ATIKU ABUBAKAR

Atiku Abubakar mutum ne wanda yake da matukar tasiri a kasar Dubai saboda karfin tattalin arziki da yake dashi a kasar ta Dubai, Dubai ita ce daular Larabawa kuma kasar da ta zamo cibiyar kasuwanci na larabawa, akwai manyan masana'antu a Kasar, kashi 10 cikin 100 na manyan masana'antu da ake dasu a kasar Dubai Atiku Abubakar yana da hannun jari a ciki


Wannan ya sa Atiku yake da matukar tasiri a Kasar, shugaban kasar Dubai kuma babban basaraken kasar Sarki Rashid Muhammad Almakhtum yana matujar ji da Atiku Abubakar, kuma ya masa alkawarin zai bashi dukkan tallafi na kudi da yake bukata idan ya kama daga dala daya ta Amurka zuwa dala biliyon daya domin ya zama shugaban Nigeria

Har yanzu Atiku yana dubai kuma tsare-tsare suke yi kan yadda zasu yaudari 'yan Nijeriya a juyawa shugaba Buhari baya don su hau karagar mulki, sunyi tanadin yin amfani da zunzurutun kudi kawai wanda idan ta kama su sayi 'yan Nigeria gaba dayansu zasu saya, kai tsaye Atiku ya samu tallafi da goyon baya daga shugaban kasar Dubai

Gwamnatin shugaba Buhari sai ta yi da gaske imba haka ba su Atiku sun yi shirin da idan lokacin zabe yazo zasu iya jijjiga gwamnatin nan idan ma basu kai ga samun nasara ba, kuma kudi ne kawai zaiyi amfani, bari ku gani a fara kanfe, ko da wasa kada shugaba Buhari da mukarrabanshi masu masa kanfe su yaudari kawunansu da cewa talakawa suna tare da shugaba Buhari, bayan talakawa suna tare da Buharin dole ayi musu wani abinda zai kara musu karfin gwiwa a tsakanin watanni uku da suka rage ayi zabe ta hanyar wayar musu da kai da kuma ihsani, idan ba haka ba su Atiku za su bada mamaki wallahi.
Daga Datti Assalafiy

No comments:

Post a Comment