Tuesday, 6 November 2018

Manyan Maluma Daga Kasar Saudiyya Sun Ziyarci Sakateriyar IZALA


A yammacin jiya Litinin tawagar manyan Malamai daga Jami'ar Ummul Qura da ke garin Makka a kasar Saudiyya wadanda suka zo Jami'ar Abuja domin yi wa alkalai da limamai daura (bita ta musamman) sun kawo ziyarar girmamawa ga Shugaban Kungiyar Izalah ta Kasa Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau a ofishin sa dake sakatariyar kungiyar a birnin Abuja.Manyan Maluman sun kawo ziyarar ne tare da rakiyar Babban jami'in da ke lura da harkokin addini a ofishin jakadancin Saudiyya (Religious Attaché) da ke Abuja Dr. Abdurrahman Bin Abdillah As-Sa'eed. Maluman sun ba wa Sheikh Bala Lau kyautar girmamawa ta musamman daga babbar jami'ar musulunci ta Ummul Qura.

Kazalika shi ma shugaban IZALA Sheikh (Dr) Bala Lau ya ba su kyaututtuka na musamman daga wannan kungiya mai tarin albarka ta JIBWIS. 

Cikin tawagar da suka zo daga Jami'ar Ummul Quran ta kasar saudiyya, karkashin jagorancin Sheikh Dr. Hasan Bin Abdilhameed Al-Bukhariy, ta hada da Dr. Ahmad Bin Mish'al Al-Gamidiy, Dr. Ahmad Bin Abdillah Ad-Durubiy, Dr. A'arif Shuj'an Al-Usaimiy, Dr. Abdulmun'im Haidar, Sheikh Muhammad Bin Salim, da Sheikh Khalid Bin Ahmad As-Sihliy.

Haka zalika Maluman JIBWIS da suka tarbi tawagar sun hada da shi kansa, Shugaban JIBWIS, Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh Yakubu Musa Hasan Katsina, Sheikh (Dr) Muhammad Kabiru Haruna Gombe, Dr. Abdullahi Saleh Usman Pakistan da Dr. Ibrahim Abdullahi R/Lemo. 

Allah ya bada ladan ziyara.
Rariya.

No comments:

Post a Comment