Monday, 5 November 2018

Maryam Gidado ta warware

Tauraruwar fina-finan Hausa da kwanannan muka ji cewa tana kwance a gadon asibiti ba lafiya, Maryam Gidado ta nuna alamun samun sauki.


Maryam din ta saka hotuna a baya inda take kwance a gadon asibiti tana rokon addu'ar masoyanta.

Saidai kuma yanzu Maryam din ta saka wannan hoton inda tace, Alhamdulillahi, wanda haka ke nuna ta fara samun sauki.

Muna fatan Allah ya bada lafiya ya sa kuma kaffarane.

No comments:

Post a Comment