Wednesday, 28 November 2018

Masu shan giya sun samu sauki yanzu an fara yinta a leda kamar ruwa

Mashaya giya sun samu sauki inda a yanzu kamfanonin yin giyar suka fara yin 'yar kara me saukin kudi ta leda, kamar dai yanda ake seda ruwan leda.

Binciken da jaridar Vanguard ta yi ta gano cewa kamfanonin yin giyar sun fara yin ta kanana a cikin leda ne saboda la'akari da yanda yanzu abubuwa suka yi tsada da kuma la'akari da karuwar yawan mata da aka samu masu shan barasar da kuma masu karamin karfi.

No comments:

Post a Comment