Wednesday, 7 November 2018

Matacce ya lashe zaben majalisar dokokin Amurka

An zabi fitaccen mai gidan karuwai kuma mai gabatar da shirin talabijin wanda ya mutu a wata jiya, Dennis Hof, a matsayin dan majalisar dokoki a jihar Nevada.


Lokacin da yake yakin neman zaben jihar, Mr Hof, mai shekara 72, ya rika kiran kansa a matsayin "Trump daga Pahrump".

Yanzu dai kwamishinonin jihar ne za su zabi wabi dan jam'iyyar ta Republican ya hau kan kujerar tasa tun da ba shi da rai.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment