Friday, 9 November 2018

Mbappe ya fadi dalilin da yasa babu wanda zai ci kyautar Ballon d'Or ta wannan shekarar tsakanin Ronaldo da Messi

Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa, Kylian Mbappe ya bayyana cewa, kyautar gwarzon dan kwallon Ballon d'Or ta wannan shekarar dan Faransa ne ya kamata ya ci ta ba Ronaldo ko Messi ba.


Ya bayyana hakane a wata hira da yayi da Express UK inda yace, har yanzu ba'a samu wanda yayi abinda yafi na Ronaldo ko Messi ba a Duniyar Kwallo, kuma koda a kakar wasa ta bana, Messi ne yafi kowa cin kwallo a nahiyar turai haka shima Ronaldo shine yafi kowa cin kwallo a gasar cin kofin zakarun turai to dole sai an samu wanda yayi fiye da haka kamin ace yayin wadannan 'yan wasa ya wuce.

Amma maganar cin kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or ta wannan shekarar, tunda a shekarar da aka buga gasar cin kofin Duniyace, dan kwallon Faransa ne ya kamata ya cita.

Ya kara da cewa sun kafa babban tarihi kuma ya kamata a yaba musu.

Yace idan dan wasan Faransa be ci kyautar ta wannan shekarar ba, ba zai ce an yi rashin adalci ba amma fa gaskiya abin kunya ne.

No comments:

Post a Comment