Monday, 5 November 2018

Mbappe ya zama dan kwallo mafi tsada a Duniya

Tauraron dan kwallon kasar Faransa me bugawa kungiyar PSG wasa, Kylian Mbappe ya zama dan wasa mafi tsada a Duniya bayan wata sabuwar kididdiga da ta fito.Rahoton wanda CIES dake kula da harkar wasan kwallon kafa ta fitar ya bayyana cewa, Mbappe ne dan wasa mafi tsada a Duniya inda darajarshi takai Yuro miliyan 189.3, sai Harry Kane, wanda da shine na daya, ke biye mishi sannan kuma sai Neymar yazo na uku.

Mohamed Salah, dan kasar Egypt ne yazo na hudu, sai kuma Messi yazo na shida, babu Ronaldo a cikin goman farko na 'yan wasan da suka fi tsada a Duniyar.

An yi amfani da alkaluman shekaru, tsawon kwantiragin dan wasa a kungiyarshi, kwazon dan wasa da kuma darajarshi a kasuwar kwallo dadai sauransu wajan fitar da wannan sunaye.

Ga sunayen goma na farko kamar haka:


Kylain Mbappe                189.3m

Harry Kane                      172.5m

Neymar                            172.2m

Mohamed Salah               151.2m

Philippe Coutinho             149.8m

Lionel Messi                      149.2m

Raheem Sterling               143.9m

Romelu Lukaku                 143.7m

Dele Alli                             142.9m

Antoine Griezmann            137.9m

No comments:

Post a Comment