Friday, 30 November 2018

Messi ya zarta Ronaldo a yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai

Tauraron dan kwallon kafar Argentina me bugawa Barcelona wasa, Lionel Messi ya zarta Ronaldo da yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai.


Kwallon da Messi ya ciwa Barca a wasan da suka buga PSV ranar Larabar da ta gabata ce ta sa yawan kwallayen da Messin ya ciwa Barca a gasar cin kofin zakarun turai suka kai 106 wanda hakan ya zarta wanda Ronaldo ya taba ciwa Real Madrid watau 105.

A yanzu dai Messi ya zarta Ronaldo a yawan kwallayen da dan wasa ya ciwa kungiya daya a gasar cin kofin zakarun turai.

Kuma ga dukkan alamu da wuya Ronaldon ya kamo Messi a sabuwar kungiyarshi ta Juve.

No comments:

Post a Comment