Monday, 5 November 2018

Messi zai kece raini da Inter Milan bayan karayar hannu

Lionel Messi na cikin tawagar Barcelona da za ta kece raini da Inter Milan a ranar Talata a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai duk da raunin da ya samu na karayar hannu makwanni biyu da suka shude.


Sanya Messi a cikin wannan tawaga ta zo da mamaki ganin yadda a farko aka yi hasashen cewa, akalla zai shafe tsawon makwanni uku na jinya kafin komawa fagen murza leda.

Ko da yake tun a makon jiya, dan wasan ya fita filin atisaye amma ba a zaci zai yi gaggawar fara buga wasa ba.

Dan wasan bai samu damar buga wasan da Barcelona ta yi raga-raga da Real Madrid da kwallaye 5-1 ba a La Liga, da kuma wanda suka casa Inter da ci 2-0.

Messi ya samu raunin ne a wasan da suka samu nasara akan Sevilla da kwallaye 4-2.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment