Thursday, 8 November 2018

Mu muka ba Man U nasarar da suka yi akan mu, basu tabuka komai ba>>Ronaldo

A wasan gasar cin kofin zakarun turai da aka buga jiya tsakanin Juventus da Manchester United, wanda Ronaldo bayan ya ci kyakyawar kwallo wadda masu sharhi ke cewa zata shiga jerin kwallayen da zasu zama mafi kyau ta wannan kakar wasa, ya je gaban 'yan kallo ya daga rigarshi inda ya nuna cikinshi me cike da murdadden nama dake nuna cewa yasha atisaye ba kadan ba.


Saidai murnar Ronaldon ta koma ciki bayan da Man U suka rama kwallon sannan kuma Sandro ya ci garin su bayan da yaji wuta daga hannun Man U.

Bayan kammala wasan, Ronaldo ya bayyanawa Sky Sport cewa wannan nasarar da Man U suka samu bafa su tabuka komai ba kawai Su, Juventus dinne suka basu ita, saboda har zuwa minti 90 na wasan sune ke rike da ragamar filin, nasarar ta Man U bama za'a kirata da sa'a ba domin ita kanta sa'a sai ka nemo ta to su kuwa basu tabuka komai ba, Inji Ronaldo.

Shima da yake magana bayan kammala wasan, dan wasan Man U wanda kuma tsohon dan wasan Juve ne, Paul Pogba ya bayyana cewa, murnar da yayi bayan kammala wasan abin ya zomai banbarakwai, an dai ga Pogban yana jinjinawa magoya bayan Juve bayan da aka kammala wasan.

No comments:

Post a Comment