Wednesday, 28 November 2018

Mu yarbawa Buhari kadai muka sani>>Inji Tinubu

Jigo a jam'iyyar APC Bola Ahmad Tinubu ya jaddada cewa, yankin yarbawa suna tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zabe me zuwa.


Yace ba zasu koma shekarun baya ba na handama da baba kere inda ya tabbatar da cewa babu wata jam'iyya a yankin yarbawan da ta wuce ta APC.

Tinubu ya bayyana hakane a wajan taron rantsar da sabon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola kamar yanda jaridar The nation ta ruwaito, ya kara da cewa, da ace PDP ta yi abinda ya kamata lokacin mulkinta da babu bukatar gyare-gyaren da gwamnatin shugaba Buhari ke yi a yanzu.

No comments:

Post a Comment