Friday, 16 November 2018

Mun gaji da sanya zumbula-zumbulan riguna: Matan Saudiyya na zanga-zanga

Wasu daga cikin matan Saudiyya sun gudanar da zanga-zangar adawa da tilasta musu sanya abaya, wadda dogowar riga ce da ke rufe tun daga sama har kasa da suke sanyawa a lokacin da za su fita bayyanar jama'a.


Wannan bore dai na gudana ne a shafukan sada zumunta da muhawara, kuma sun sanyawa maudu'in suna ''sanya abaya a bai-bai'', tare da wallafa hotunan mata sanye da abaya da kuma nikabin rufe fuska wadda suke korafin tana takura musu.

A watan Maris da ya wuce, Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman bin Abdul'azeez al-Su'ud ya bayyana cewa sanya doguwar abayar ba tilas ba ne ga matan kasar.

Kusan mutane 5,000 ne daga ciki da wajen kasar suka ta tsokaci kan batun a shafin Twitter.
Wace sutura matan Saudiyya za su sanya?

Gwamman shekaru da suka gabata, hukumomin Saudi na da tsaurin ra'ayi kan suturar da matan kasar ke sanyawa wadda za ta rufe baki dayan jikinsu a bainar jama'a, inda suke sanya abaya matukar musulmi ne.

Amma a watan Maris Yarima Muhammad ya ce mata ba sa bukatar sanya zumbuleliyar rigar, suna bukatar a dama da su a fagen suturar zamani matukar kayan ba sa nuna tsiraici don haka ba lallai sai sun sanya abaya ba.

A wata hira da gidan talabijin na CBS Yariman ya ce "dokokin addinin musulunci a bayyane suke, addinin ya amince mata su sanya tufafin da suka kaimuradi, abu mai muhimmanci shi ne dole su suturta jikinsu, kamar yadda aka umarci maza su aikata hakan."

Bin Salman ya kara da cewa, "Hakan ba yana nufin lallai sai sun sanya abaya ko bakin nikabin rufe fuska ba. Baki dayan zabi yana ga matan su zabi irin suturar da suke muradin sanyawa."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment