Monday, 5 November 2018

Mutum mutumin Mo Salah ya jawo ce-ce-ku-ce a Masar

Mutum mutumin dan wasan Liverpool da masar Mohamed Salah wanda aka kaddamar a kasarsa ta haihuwa ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.


An kaddamar da mutum mutumin ne a wurin wani biki na Matasan Duniya da aka gudanar da Sharm al-Sheikh ranar Lahadi.

Mutum mutumin ya nuna dan wasan hannaye a bude kamar yadda yake yi idan yana murnar zura kwallo.

Sai dai mutane da dama sun ce mutum mutumin ya yi kama da na mawaki Leo Sayer ko kuma Marv na cikin fim din Home Alone.

 Hoton Hakkin Mallaka @MoSalahFacts@MOSALAHFACTS

Mutum mutumin na Salah ya bi jerin mutum mutumin 'yan kwallon kafa da aka kaddamar a kasashe daban-daban wadanda suka sanya magoya bayansu na cewa ba su yi kama da su ba.

Wannan mutum mutmin ya sa an riga kwatanta shi da na Cristiano Ronaldo wanda aka rika zolaya bayan an kaddamar da shi a filin jirgin saman Madeira a shekarar da ta wuce.

Emanuel Jorge da Silva Santos, w andaya sassaka mutum mutumin, ya bayyana bacin ransa kan sukar da aka rika yi masa a shafukan intanet bayan ya sassaka shi.

Taron kungiyar matasan, inda aka kaddamar da mutum mutumin Salah, ya samu halartar dubban mutane, ciki har da shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi.

Matasa sun soma taron ne, wanda shi ne karo na biyu, domin wanzar da zaman lafiya a Masar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment