Friday, 30 November 2018

Neymar ya zama dan kasar Brazil da yafi yawan cin kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai

Tauraron dan wasan Brazil dake bugawa kungiyar PSG wasa, Neymar ya zamo dan wasan da ya fi kowane dan wasan kwallon kasar ta Brazil yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai.


Neymar ya kai ga wannan nasarane a wasan da PSG ta buga da Liverpool a ranar Larabar da ta gabata inda ya ciwa PSG din kwallo, yanzu dai yawan kwallayen da Neymar din ke da su a gasar cin kofin zakarun turai sun kai 31 inda hakan yasa ya shiga gaban Kaka me yawan kwallaye 30.

Mutum na uku me yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai dan kasar Brazil shine Rivaldo me yawan kwallye 27.

No comments:

Post a Comment