Tuesday, 6 November 2018

Nigeria: Kungiyoyin kwadago sun janye yajin aiki


Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun janye yajin aikin gama garin da suka shirya tsunduma a ranar Talata.Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da kungiyoyin suka cimma da masu ruwa da tsaki a kasar a kan batun karin mafi karancin albashin ma'aikata na naira dubu 30 bayan taron da suka yi a daren ranar Litinin.

Comrade Nasiru Kabir, sakataran tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriyar wato ULC, ya shaida wa BBC cewa, gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar da suka fara na mafi karancin albashin ma'aikata.


Comrade Nasiru, ya ce dama kungiyoyin sun yi niyyar tafiya yajin aikin ne saboda gazawar gwamnati na cika alkawarin da ta daukar musu a kan albashin.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar ta ULC, ya ce gwamnatin tarayyar ta yi alkwarin tursasa wa gwamnatocin jihohin kasar a kan su biya karin albashin da aka amince da shi.


Game da batun lokacin da za a fara biyan sabon albashin kuwa, comrade Nasiru ya ce, sai yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin ta zama doka tukunna.

Ya ce, sabon tsarin albashin zai shafi dukkan ma'aikata ne ba na gwamnati ba ne kawai, zai shafi ma'aikatan kamfanoni da sauransu, ma'ana zai shafi duk wani mutum da ake kira ma'aikaci.

Kungiyoyin dai sun sha alwashin tafiya yajin aikin ne a ranar Talata saboda rashin amincewa da karin albashin naira dubu 22 da 500 da gwamnoni suka ambata a baya.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment