Friday, 9 November 2018

Oshiomhole na kan hanyar dawowa Najeriya

Rahoton dake fitowa daga jaridar The Cable na cewa, shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole yanzu haka yana kan hanyar dawowa Najeriya daga kasar Ingila inda yaje hutu.Kamin nan dai an samu rahotannin cewa Oshiomhole din ya fice daga Najeriyane saboda matsin lambar hukumar DSS da gwamnoni akan sai ya sauka daga mukaminshi.

Kamin wancan rahoto an ta watsa wannan hoton na Oshiomhole da matarshi inda rahotanni suka bayyana cewa an dauki hotonne a can kasar waje inda suka je shakatawa.

No comments:

Post a Comment