Saturday, 17 November 2018

PDP Ta Yi Watsi Da Ni>>Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya koka kan cewa Jam'iyyar PDP ta yi watsi da shi inda ya yi barazanar kin marawa dan takarar Jam'iyyar na Shugaban kasa, Atiku Abubakar.


Toshon mai taimakawa tsohon Gwamnan, Umar Danjani ya ce tun bayan da aka kammala zaben fidda gwani na 'yan takarar Shugaban kasa wanda Atiku Abubakar ya lashe, jam'iyyar ta jefar da Sule Lamido gefe daya inda ake gudanar da harkokin Jam'iyyar ba tare da shi ba.
Rariya.

No comments:

Post a Comment