Saturday, 3 November 2018

Ronaldo ya ci kwallaye fiye da wasannin da ya buga a shekarar 2018

Tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ya sake yin wata bajinta da ta dauki hankulan Duniyar kwallo, idan aka hada yawan wasannin da ya buga da kwallayen da yaci a wannan shekarar 2018, Ronaldo yaci kwallaye fiye da wasannin da ya buga.


A Madrid da Juventus, Cristiano Ronaldo ya buga wasanni 35 a wannan shekarar sannan kuma ya ci kwallaye 36.

Haka kuma a wata kididdiga da Opta suka fitar ta nuna cewa, Ronaldo be cika bayar da fasin din kwallo ba amma kuma shine ke da kashi 46 cikin 100 na hare-haren cin kwallo da kungiyar takai a kakar wasa ta bana.

Ronaldo dai ya kuma zama mutumin da ya fi daukar hankalin Duniya bayan da ya zama mutum na daya da yafi yawan mabiya a shafin Instagram inda ya zarce wadda ke rike da wannan kambu na tsawon lokaci watau, Selena Gomez.

Selena dai ta dan kwana biyu bata hau shafin na Instagram ba tun bayan wani sako data fitar inda ta rubuta cewa zata je ganin likita akan ciwon tabin hankali dake damunta.

Tun dai kamin Ronaldon ya zama na daya a mabiya a shafin Instagram, inda za'a hada mabiyanshi na sauran shafukan zumunta da ana sauran taurarin Duniya dama yafi su yawan mabiya.

No comments:

Post a Comment