Friday, 9 November 2018

Ronaldo ya nemi afuwar 'yan Manchester United

A wasan da aka buga na cin gasar kofin zakarun turai a tsakiyar makonnan tsakanin Juventus da Manchester United wanda aka tashi Man U na cin Juve 2-1, Ronaldo ya ci kwallo daya kuma irin yanda yayi murnar cin kwallon ya jawo cece-kuce.


Ronaldo dai ya je gaban 'yan kallo ya daga rigarshi inda ya nuna murdadden naman cikinshi wanda hakan ya jawo wasu basu ji dadi ba.

Saidai Ronaldon ya bayar da hakuri ga magoya bayan Man U wanda hakan ke nufin yayi nadamar abin da ya aikata. Ya saka wannan hoton na sama a dandlinshi na sada zumunta wanda ya dauki hankula.

No comments:

Post a Comment