Thursday, 29 November 2018

SABON ALBASHIN 'YAN SANDA: Shugaban 'yansanda zai tashi da naira miliyan 3.3 a matsayin alawus din muhalli

Sabon tsarin albashin ‘yan sanda da Shugaba Buhari ya amince da dabbaka shi a jiya ya nuna cewa babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya (I-G) zai karbi alawus din mahalli da adadinsa ya kai Naira miliyan 3.3 a shekara.


Masu mukamin DIG kuma za su tashi da Naira miliyan 3.02, inda su kuma masu mukamin AIG za su tashi da Naira miliyan 2.7 a shekara a matsayin alawus na rage radadin kudin hayar mahalli.

Kamfanin dillacin labarai na Nigeriya ta gano hakan ne daga wata takardar amincewa da kunshin sabon tsarin albashin da aka aika ofishin babban sufeton ‘yan sandan na kasa, sai dai takardar bata bayyana yadda tsarin albashin zai kasance ba.

Takardar alawus din kudin hayar mahallin ta bayyana cewa ‘yan sanda masu mukamin kwamishina za su tashi da Naira miliyan 1.5 a shekara, DCM kuma zai tashi da N531,000, sai ACM kuma zai samu N483,000.

CSP zai samu N419,000, SP kuma zai tashi da N342,000, DSP zai samu N321,000, ASP I zai samu N296,000, shi kuma ASP II zai samu N271,000 a matsayin kudaden da za su rage musu radadin biyan kudin hayar mahalli.

Dan sanda mai mukamin Insifekta I za samu N254,000, Insifekta II za samu N167,000, Samanja kuma zai samu N119,000, Sajan kuma za a biya shi N96,000, sai Kofur da zai karbi N88,000 a shekara.

‘Yan sandan konsitabul na 1 zai karbi N86,000, mai mukamin konsitabul na 2 zai samu N84,000 a sabon tsarin albashin da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Wannan dai bangaren alawus din albashi ne kawai na kunshin sabon albashin na ‘yan sanda da za su samu a tsittsinke cikin watanni 12 na shekara a matsayin alawus na mahalli.
Rariya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment