Wednesday, 7 November 2018

Sakamakon wasannin cin kofin zakarun turai da aka buga yau: Ronaldo ya ciwa Juve kwallo ta farko

A wasannin cin kofin zakarun turai da aka buga yau, Laraba, Manchester United ta bi Juventus har gida ta lallasa ta da ci 2-1.

Har aka kai ga hutun rabin lokaci babu wanda yaci kwallo, sai bayan da aka dawone, wasa ya kara yin zafi sannan Ronaldo ya ciwa Juve kwallo ta farko a gasar cin kofin zakarun turai, dama dai tun dazu da yamma me horas da 'yan wasa na Juve ya bayar da tabbacin cewa yau Ronaldo zai ci kwallo a hirar da yayi da Eurosport.

Saidai Juan Mata ya ramawa Man U kwallon sannan kuma daga baya Alex Sandro ya ci garinsu, Juventus, a haka aka tashi wasan.

Sauran  sakamakon wasannin da aka buga yau sune:

Bayern Munich 2

Athens 0

Benfica 1

Ajax 1

Lyon 2

Hoffenheim 2

Man City 6

Donetsk 0

CSKA Moscow 1

Roma 2

Plzen 0

Real Madrid 5

Valencia 3

Young Boys 1


No comments:

Post a Comment