Saturday, 10 November 2018

Saura kiris: PDP ta yi nisa wajen zawarcin wani gwamnan APC kafin zaben 2019

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) shiyyar jihar Legas ta bayyana cewa tuni shirye-shirye suka yi nisa tsakanin ta da gwamnan jihar ta Legas Akinwumi Ambode da sauran 'yan jam'iyyar da dama don gani ta zawarto su zuwa jam'iyyar daga All Progressives Congress (APC).


Jam'iyyar ta PDP ta ce tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta fahimtar da dukkan wadanda aka batawa rai a APC din sun dawo a jam'iyyar su tare kuma da basu tabbacin kyakkyawan adalci a sabuwar jam'iyyar ta su idan suka amince.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP a jihar legas Mista Taofiq Gani ya fitar dauke da sa hannun sa inda yace yanzu haka ma sun soma tattaunawa da wasun su.

A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta soma sakin sunayen wadanda za suyi takarar kujerun gwamnoni a jahohin Najeriya ashirin da hudu da za'a gudanar da zabukan shekarar 2019.

Haka zalika mun samu cewa hukumar zaben har ila yau ta soma fitar da sunayen wadanda za suyi takarar kujerun 'yan majalisun jahohin tarayyar Najeriya dukkan su da za'a gudanar da zabukan su a shekarar ta 2019.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment