Tuesday, 13 November 2018

Shahararren marubuci Stan Lee ya mutu

Marubucin litattafan nishadi da jarumta Stan Lee, wanda ya kawo sauyi a kan yadda ake shirye fina-finan a masana'antar hollywood ya rasu a Los Angels.


Stan Lee mai shekara 95, a lokacin da ya ke kan ganiyar aikinsa, shi ya kirkiri labarin fina-finan nan na ban dariya, da nuna bajinta wato Spiderman da The incredible hulk da kuma Captain America.

Gidajen sinima a fadin duniya sun yi cinikin sama da dala biliyan 20 ta hanyar wadanan fina-finai.

Shugaban kamfanin shirye fina-finai na Walt Disney, wanda yanzu haka ya mallaki Marvel ya ce Stan Lee wani mutum ne na daban, kamar yadda jaruman fina-finan da ya kirkira suke.

Ya kuma ce Stan Lee dan baiwa ne da ya ke da basirar nishadantarwa da kuma karfafa wa wasu kallo da bibiyar fina-finai ko ayukansa gwiwa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment