Monday, 26 November 2018

Sheik Gumi Ya Gargadi Buhari Kan Tsare El Zakzaky

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheik Ahmad Gumi ya gargadi Shugaba Muhammad Buhari bisa yadda gwamnatinsa ke ci gaba da tsare Shugaban Kungiyar 'Yan Shi'a, Malam Ibrahim El Zakzaky duk da yake kotu ta bayar da belinsa.


Sheik Gumi ya kara da cewa El Zakzaky ya fara bayar da hadin kai ga gwamnati kafin daga baya al'amurra su runcabe inda ya jaddada cewa dole gwamnati ta mutunta hukumcin kotu kan sakin El Zakzaky.
Rariya.

No comments:

Post a Comment