Tuesday, 27 November 2018

Shugaba Buhari ya fasa zuwa hutu dan jimamin rayukan da aka rasa a yaki da Boko Haram

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fasa zuwa hutun kwanaki 5 da ya kamata yaje dan alhinin rayukan da aka rasa a yaki da kungiyar Boko Haram.


Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ya kamata shugaba Buhari yaje hutu daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba wanda yayi niyyar yi a mahaifarshi ta Daura dake jihar Katsina amma ya fasa.

Dama dai a jiya rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya fasa zuwa ziyarar da yayi niyyar kaiwa Edo inda yanzu zai je Borno ne inda zai kaddamar da wani taron tsaro ya kuma yiwa sojojin dake bakin daga jawabi ranar 28 ga watannan.

No comments:

Post a Comment