Friday, 2 November 2018

Shugaba Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki daga jihar Naija

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin masu sarauta da 'yan siyasar jihar Nija a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja, gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, mataimakimshi da tsohon gwamnan jihar, Dr. Mu'azu Babangida Aliyu na daga cikin wanda suka kaiwa Buharin ziyara.Akwai kuma Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da sauran masu rike da sarautar gargajiya.

Da yake jawabi a gurin taron, shugaban kasa, M. Buhari ya bayyana cewa rashin amincewa da kasafin kudi da majalisa ke yi da wuri ne ke kawo tsaiko wajan yin ayyukan raya kasa, yace amma duk da haka suna kokarin ganin sunyi iya bakin kokarinsu

Ya kara da cewa, abin ba ya mai dadi ganin cewa majalisa na daukar watanni 7 kamin ta amince da kasafin kudi kuma ya bayyanawa 'yan majalisar hakan.

Buhari ya kara da cewa, irin wannan ziyara ta manyan mutane takan kara mai kwarin gwiwa akan ayyukan da ya kewa al'umma.

No comments:

Post a Comment