Monday, 26 November 2018

Shugaba Buhari ya soke ziyarar da yayi niyyar kaiwa jihohin Benue da Edo dan ziyartar jihar Borno

Domin jimamin harin da aka kai da yayi sanadiyyar mutuwar sojoji da dama a jihar Borno, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fasa ziyarar da yayi niyyar kaiwa jihohin Benue da Edo gobe, maimakon haka zai kai ziyara jihar ta Borno ranar Laraba.


Me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka.

No comments:

Post a Comment