Friday, 30 November 2018

Shugaba Buhari zai je kasar Poland ranar Asabar

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai je kasar Poland ranar Asabar me zuwa idan Allah ya kaimu inda zai halarci taron da za'ayi akan canjin yanayi a babban birnin kasar, Katowice.


Sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a gurin taron da zai bayyana gudummuwar da Najeriya ke bayarwa wajan magance dumamar yanayi.

Sannan kuma zai yi ganawa ta musamman da shugaban kasar ta Poland, Andrzej Duda.

Wadanda zasu wa shugaban rakiya zuwa kasar ta Poland sune gwamnonin jihohin Enugu,Kogi, Naija da sauran wasu manyan ma'aikatan gwamnati.


No comments:

Post a Comment