Saturday, 10 November 2018

Sule Lamido Uba Ne, Duk Wanda Ya Ci Mutuncinsa Tamkar Mutuncina Ya Ci, Inji Gwamna Badaru

Da ranar jiya Juma'a Gwamnan jihar Jigawa, Alh. Muhd Badaru Abubakar, ya karbi bakoncin tsofin wakilan kungiyar Sule Lamido social media, daga kananan hukumomi 27 dake fadin jihar.


Shugaban tafiyar, Engr, ya bayyana wa gwamnan, wannan ziyara ce da  wannan 'yan tsohuwar waccar kungiya suka kawo wa gwamnan, da kuma tabbatar da biyayyarsu ga wannan Gwamnatin, na ganin irin aiyukan alkhairi da take bulbulawa. Sa'id ya bayyana nawa gwamnan, cewa sun kafa sabuwar kungiya domin aiki tukuru, (APC NEW MEDIA FRONT)/wajen ganin wannan adalar gwamnati ta kai ga nasara.

Gwamnan jihar Jigawa, Alh. Muhammad Badaru Abubakar, ya yaba wa wannan 'yan kungiya, bisa irin wannan hangen nesa da sukai tun wuri.

Gwamnan ya ja hankalin 'yan kungiyar da su guji cin mutuncin shugabannin su, domin "Sule Lamido ubana ne, in ka zagi Sule Lamido wallahi ni ka zaga" in ji Gwamna Badaru.

Gwamnan ya ce ya yafewa duk wani wanda ya bata wa a baya, kuma ya nemi yafiyar duk ka wanda ya batawa shi ma.

Daga karshe Gwamnan ya yi wa kowa fatan alkhairi, da kuma zage damtse domin aiki tukuru.
Rariya.

No comments:

Post a Comment