Wednesday, 28 November 2018

Super Falcons ta tsallake zuwa wasan karshe

Kungiyar wasan kwallon kafar mata ta Najeriya, Super Falcons, za ta buga wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta mata na 2018, tsakaninta da takwararta ta Afirka ta kudu.


Super Falcon ta lallasa kungiyar kwallon kafar mata ta Kamaru da ci hudu da biyu a bugun fenareti ranar Talata.

Yanzu dai kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya za ta kare kambunta ne a wasan karshe tsakanin ta da kungiyar kwallon kafar mata ta Afirka ta kudu.

Kungiyar ta Afirka ta Kudu ta yi nasarar kai wa wannan zagaye ne bayan ta lallasa kungiyar kwallon kafar mata ta Mali da ci biyu ba ko daya a wasan kusa da na karshe.

Nasarar da Super Falcon din ta samu ta sa ta kafa tarihin zuwa dukkanin gasar cin kofin duniya ta mata wadda a nan gaba za a buga karo na takwas.

Ita kuwa Afirka ta Kudu, wannan shi ne karon farko da za ta je gasar ta duniya.

A ranar Asabar mai zuwa ne za a buga wasan neman na uku tsakanin Kamaru da Mali, kuma duk wanda ta yi nasara a cikin su za ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta duniya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment