Wednesday, 7 November 2018

TA BARKE DA KUKAN FARIN CIKI BAYAN DA TA YI ARBA DA SHUGABA BUHARI

A jiya Talata ne dai Jagorori da Shugabannin wata Babbar Coci ta Kiristoci (COCIN) suka kaiwa Shugaba Buhari Ziyara. Bayan doguwar Tattaunawa na tsawon lokaci Shugaban kasar Shuwagabannin (COCIN) sun Jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa irin yadda yake Gudanar da Shugabancinsa tare da yi Masa addu'o'in samun cigaba da kuma karin Nasara a mulkinsa. 


Bayan kammala Ganawar ta su, Yayin da aka je Daukar hoto, Kwatsam sai aka hango daya daga cikin Manyan shugabannin na addinin kirista, ta barke da kuka, har da hawayenta share-share.

Ko da kuwa aka tambaye ta, dalilin yin kukan na ta, sai ta ce "Kukan farin ciki ne take Na yin Tozali da Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi a Karon Farko na Rayuwarta." Ta kara da cewa "Sakamakon Shi Buharin Irin yadda Allah ya yi shi daban da Sauran mutanen Najeriya. Yana da Gaskiya, Ga Rikon Amana, Sannan yana nuna Dattako da iya tafiyar da Mulki, wanda irin su a Duniya ba su da yawa" 

Ta kara da cewa "Matukar 'yan Najeriya na da Ra'ayi irin na ta, To a bar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta Mulkin kasar nan har Illa Masha Allah".
Rariya.

No comments:

Post a Comment