Friday, 30 November 2018

Tabbas Mun Ci Karfin Boko Haram, Shure-shure Suke Yi>>Minista Dambazau

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne, Ministan harkokin cikin gida na kasar nan, Janar Abdurrahman Bello Dambazau, CFR, (mai ritaya), ya kaddamar da ginin wata katafariyar cibiya, wacce hukumar shige da ficeza ta gina domin adana bayanan shige da fice a kasar nan. 


Bayan taron ne Ministan ya yi wa LEADERSHIP A YAU JUMA’A karin haske a kan dalilin kafa wannan cibiya da kuma halin da ake ciki a yakin da kasar nan ke fafatawa da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Minista Dambazau, ya ce, dalilin kafa wannan waje shi ne, “adana dukkanin bayanai a waje guda, na farko dai domin kare dukkanin bayanan mu, abu na biyu kuma shi ne, samar da hanya mafi sauki na samun bayanan, sannan kuma yin hakan zai sa a sami gamsasshen tsari na tattara dukkanin bayanai. Wadannan su ne mahimman dalilan kafa wannan cibiya.

“Kamar yanda na fada ne, daya daga cikin babban kalubalen da ke fuskantar mu a halin yanzun shi ne, ayyukan ‘yan ta’adda a kan iyakokin kasar mu, ta yanda suke samun daman shigowa da makamai, suke samun daman shigowa da miyagun kwayoyi, da ma safarar mutane, sai kuma yanda ta hakan ne ‘yan ta’adda suke samun mafakan su.

“Duk wadannan miyagun ayyuka mutane ne ke aiwatar da su a kan iyakokin mu, don haka, ta hanyar sanya tsaron da ya dace za mu iya bambancewa a tsakanin mutumin kwarai da kuma wanda ba na kwarai din ba. Kamar kuma yanda na fada ne, za mu samar da cikakken hadin kai da ‘yan sandan kasa da kasa.

“Sannan kuma ta hakan zai sanya mu iya samun bayanan duk wani dan adam, da zai shigo cikin kasar nan ko kuma ya fita daga cikin ta. Da wannan kuma za mu iya samun bayanin duk wani dan Nijeriya wanda yake aikata wata barna. Wannan kuma zai taimaka mana matuka wajen samar da tsaro a kasar mu.

“Ko shakka babu, mun ci karfin Boko Haram, kar ku manta, a shekarar 2015, da wannan gwamnatin ta zo, kimanin kananan hukumomi 14 duk tutocin Boko Haram ne ke filfilawa a cikin su. Amma lamarin ba haka ne ba a yanzun. Abin da ke faruwa a halin yanzun, lamari ne da ya shafi tafkin Cadi, shi kuma wannan tafkin Cadin, mallaki ne da ke karkashin kasashe hudu, Nijeriya, Kamaru, Nijar da kuma Cadi. Hakan ne kuma ya sanya aka kafa ma yankin hukuma na shi na kanshi. 

Don neman magance wannan matsalar ne ya sanya, a maganan nan da nake yi da ku, Shugaban kasarmu a yanzun haka yana can Cadi domin neman mafita a kan wannan mahimmin al’amari, domin abin shi ne, wasun su suna kaddamar da hare-haren na su ne daga yankunan kasashen Cadi da Nijar.

“Don haka, domin magance lamarin akwai bukatar yunkuri daga wadannan kasashen da suke da hannu a kan tafkin na Cadi, wannan ne kuma dalilin da ya sanya a yanzun haka, Shugaban kasa yake a kasar ta Cadi, domin tattaunawa,”in ji shi.

Wannan dai yana zuwa ne kimanin makwanni biyu da kashe wasu Sojoji da ‘yan ta’addan na Boko Haram suka yi, a wani sansanin Sojoji da ke Metele.

Tuni dai, Shugaba Buhari ya soke karamin hutun da ya yi nufin zuwa, ya shiga tattaunawa da hukumomin tsaro na kasa, yana mai alkawarin kawo karshen ‘yan ta’addan.

No comments:

Post a Comment