Saturday, 10 November 2018

Talauci 'ya hana 'yar majalisa budurwa biyan kudin haya'

Budurwa mafi karancin shekaru da ta lashe zaben majalisar dokokin Amurka ta ce ba za ta iya biyan kudin hayar gidan da za ta kama a birnin Washington DC ba.


Alexandria Ocasio-Cortez ta shaida wa New York Times cewa za ta jira zuwa watan Janairu lokacin da za ta soma daukar albashi a majalisa kafin ta samu kudin biyan haya.

Washington DC na cikin birane 10 mafi tsadar haya a duniya. Ana biyan kimanin $2,160 domin kama gida mai daki daya a kowanne wata, a cewar jaridar according to Business Insider.

Yanzu dai an soma yi mata lakabi da "budurwar da ta zama 'yar majalisa".

Sai dai ranar Juma'a mai gabatar da shirye-shiryen Fox News Ed Henry ya yi ikirarin cewa ba gaskiya 'yar majalisar - mai shekara 29 - take fada ba domin kuwa ta taba sanya wasu tufafin dubban dala lokacin da aka yi hira da ita a wata mujalla.

Ms Ocasio-Cortez ta yi masa raddi a shafinta na Twitter inda ta ce ta aro kayan ne ta sanya domin mujallar ta dauki hotonta.

Kalaman da ta yi cewa - "Yanzu dai ina ta fama da talauci kuma ina jira watan Janairu domin na samu kudin" - sun sa masu amfani da shafin Twitter da dama sun tausaya mata.

"Abin da Alexandria Ocasio-Cortez fada cewa ba za ta iya biyan kudin hayar gida a Washington DC ba ya sa na ji daban kuma gaskiya na tausaya mata," in ji wani mai amfani da Twitter.

Ms Ocasio-Cortez za ta bi sahun 'yar Republican Elise Stefanik, mai shekara 34, da kuma 'yar Democrat Ilhan Omar, mai shekara 36, da sauransu, domin kasancewa matasan matan da suka lashe zaben majalisar dokokin.

Za ta wakilci gunduma ta 14 da ke birnin New York bayan ta yi yakin zabe kan yadda za ta magance batutuwa irinsu talauci da rashin daidaito wurin rabon arzikin kasa da matsalolin 'yan gudun hijira.

Iyayenta 'yan asalin Puerto Rico ne ko da yake an haife ta a garin Bronx na Amurka.
Ta bayyana kanta a matsayin mai matsakaicin samu kuma ta yi aiki a wani gidan sayar da abinci har zuwa farkon 2018.

Bayanan da Ms Ocasio-Cortez ta wallafa sun nuna cewa ta samu $26,500 a shekarar da ta wuce.
BBChausa

No comments:

Post a Comment