Friday, 2 November 2018

Tare muka yi makaranta da Shehu Musa 'Yaradua>>Shugaba Buhari

Wadannan hotunan shugaban kasa, Muhammadu Buharine lokacin da yake amsar takardar shedar jarabawar WASCE a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja a yau, Juma'a a lokacin da yake karbar shaidar jarabawar ya yabawa hukumar shirya jarabawar inda yace duk da tsawon shekarun da aka shafe amma sun rike gaskiya a aikinsu.Buhari ya kara da cewa da bai rubuta jarabawar ba babu yanda za'a yi a matsayinshi na soja ya halarci makarantun horas da soji na kasar Amurka. Yace shi da marigayi janar Shehu Musa 'Yaradua tare suka yi jarabawar ta WASCE a shekarar 1961 wanda daga nan ne suka shiga aikin soja.

Yace tun daga firamare har zuwa sakandire tare suka yi da 'Yaradua.
No comments:

Post a Comment