Thursday, 1 November 2018

Tattalin arzikin Najeriya ya samu tagomashi, zamu kara ingantashi>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattalin arzukin Najeriya ya na kara habaka kuma gwamnatinshi zata ci gaba da yin kokari dan kara ingantashi.


Shugaban ya bayyana hakane a yau, Alhamis lokacin da yake karbar sabon jakadan kasar Denmark a Najeriya, Jesper Kamp, kamar yanda sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ta bayyana.

Shugaban ya kara da cewa, yaji dadin yanda dangantakar Najeriya da Denmark ke kara karfi.

Sauran sabbin jakadun kasashen da Buharin ya amsa a fadarshi sune na kasashen Belarus, Pakistan da Senegal.

No comments:

Post a Comment