Thursday, 8 November 2018

Tsaurin ido: Minista mai ci ya rufe ofishin kamfen din Buhari/Osinbajo a jihar sa

An zargin ministan sadarwa, Adebayo Shitu, da rufe ofishin yakin neman zaben shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo da ke Ibadan.


Ministan ya yi haka ne bayan burinsa na samun tikitin takarar gwamnan jihar Oyo a inuwar jam'iyyar APC bai cika ba.

Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ne ya yi watsi da takarar ministan bayan samun sa da laifin kin yin bautar kasa lokacin da ya kammala karatun jami'a.

A satin da ya gabata ne aka ga wata babbar motar daukan kaya, a ginin MBO da Ofishin kamfen din Buhari/Osinbajo, na debe dukkan wasu kaya mallakar ministar zuwa wurin da babu ya sani.

Ma su aiki a ofishin yakin neman zaben sun ki cewa komai lokacin da manema labarai su ka tunkare su.

Sai dai wata majiya da ke da kusanci da mutumin da ya mallaki ginin da ofishin kamfen din ya ke ya ce tun a watan Satumba kudin hayar ofishin ya kare tare da bayyana cewar alamu sun tabbatar da cewar ministan ba zai kara biyan kudin hayar wata shekarar ba.

"Da kansa ya sa a dauke duk kayan da ke cikin ofishin, ba bu wanda ya matsa ma sa a kan batun karewar kudin haya," a cewar majiyar mu.

Sai dai mai magana da yawun ministan, Mista Tajudeen Kareem, ya ce an dauke kayan domin canja su da wasu sabbi.

Da aka yi masa zancen cewar dama kudin hayar ofishin ya kare, sai Kareem ya ce, "bani da masaniya a kan hakan, ni abinda na sani shine akwai maganar canja kayan katakon ofishin kafin ziyarar yakin neman zaben shugaba Buhari da kwanan nan za a fara."
Legit.ng.


No comments:

Post a Comment