Monday, 5 November 2018

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Farfesa Hafizu Zai Yi Takarar Gwamna A PRP

Tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Kano mai murabus Farfesa Hafizu Abubakar ya ziyarci ofishin shugabacin jam’iyyar PRP reshen Jihar Kano tare da rakiyar magoya bayansa inda ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya shigo jam’iyyar tare da shiga cikin sahun masu neman tsayawa takarar Gwamnan Kano a karkashinta.


Farfesa Hafizu Abubakar  ya shigo jam’iyyar ne don manufofinta da yake fatan za a sami cika burin wanda ya kafa jam’iyyar tun a baya dan ceton al’umm daga danniya. Ya ce bai ga jam’iyya a halin yanzu da take da tsari irin PRP ba, wanda tun yana dalibi a 1978 aka kafata har ma suna zuwa tarukan jam’iyyar.

Tsohon mataimakin Gwamnan na Kano, Farfesa Hafizu Abubakar ya yi nuni da cewa dukkan yunkuri da aka yi na baya suka jawo kafa jam’iyyar PRP dan ceto al’umma sun bayyana a yanzu shi ya sa ya taho jam’iyyar don hada kai da bada gudummuwa dan ceto al’ummar Kano daga danniya, tunda tsari ne  na ci gaba da farfado da al’umma sun shiga cikin ‘yan uwa don bada gudummuwarsu.

Farfesa Hafizu Abubakar ya ce shi a tsarin siyasarsa ba cin mutunci, ba kuma wata magana ta gida-gida ko a ce Hafiziyya ko wani abu da yayi kama da haka, magana ce ta PRP a ciccibata  dan kawo gyara, saboda matsaloli sun addabi al’umma, an  bar Arewa a baya a ilimi da sauran fannoni na ci gaban al’umarta, wajibi ne su shigo su dasa ginshiki ta ci gaban al’umma. duk mai kishin Kano ya zo ya shiga PRP a yi tafiyar nan da shi, su kuma shugabannin jam’iyyar su tsaya akan manufa ta akida kuma su zasu bada goyon baya matukar ba’a kaucewa tsari da manufofin da aka gina jam’iyyar akai ba.Farfesa Hafizu Abukar wanda yana tare da dukkan magoya bayansa yayin ziyarar da yace dukkansu ya taho da su cikin jam’iyya da suka hada da Alhaji Shehu Haza da Dakta Bukari da sauran wadanda suka rike mukaman masu bashi shawara yana Gwamnati kafin yayi murabus.
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment