Saturday, 10 November 2018

Ummi Zeezee ta zama shugabar mata ta kungiyar kanfe din Atiku

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta zama shugabar mata ta kungiyar kamfe din dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shugaban gidauniyar tallafawa marasa galihu ta Atikun, Atiku Cares, Ambasada Aliyu Bn Abbas ne ya bayyana haka.


A sanarwar da ya fitar ta shafinshi na sada zumunta ya taya Ummi murna sannan yace suna fatan zata yi aiki tukuru ta kuma bi gida-gida dan tallata Atiku.

Muna tayata murna.

No comments:

Post a Comment