Sunday, 4 November 2018

WAEC ta musanta ikirarin fadar shugaban kasa akan samakon jarabawar Buhari

Ga dukkan alamu dai duk da cewa hukumar shirya jarabawar WAEC ta baiwa shugaba Buhari sakamakon jarabawarshi Duniya ta gani amma cece-kuce be kare ba akan sakamakon jarabawar.


An samu banbancin magana akan yanda aka baiwa Buharin sakamakon jarabawarshi tsakanin hukumar WAEC da kuma fadar shugaban kasa.

Me magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya shaidawa jaridar Punch cewa fadar shugaban kasar ba ta bukaci WAEC ta baiwa Buhari sakamakon jarabawarshi ba, hukumar ce da kanta taga dacewar hakan bayan da ta karanta irin cece-kucen da ake ta yi akan sakamakon jarabawar ta kuma kawowa Buharin abinshi dan radin kanta.

Saidai kuma WAEC din ta musanta wannan magana ta fadar shugaban kasa a wata hira da tayi da jaridar Punch din dai inda tace, Buhari ne da kanshi ya bukaci hukumar ta bashi sakamakon jarabawar tashi, domin dama shi kadai ne ko kotu ke da hurumin tambayar a basu sakamakon jarabawar kuma da ace be tambaya ba babu yadda za'a yi su bashi.

Haka kuma akwai cece-kuce akan hoton Buhari da aka gani akan sakamakon wanda sabon hotone inda mutane suka ta tambayar yaya haka?

Shima hukumar ta warware matsalar inda tace ba sabon sakamakon jarabawane suka ba Buhari ba amma kwafi ne ko kuma shaidar dake tabbatar da cewa yayi jarabawar kuma a lokacin da mutum ya batar da sakamakon jarabawar nashi yana da damar tambayar WAEC din ta bashi kwafin wani kuma a lokacin da yake bukatar hakan zai bayar da hotunan fasfo na kwanannan guda biyu.

Haka kuma hukumar jarabawar tace dalilin da yasa ba'a ga sakamakon wasu darussa akan sakamakon da suka baiwa Buhari ba shine, yanzu sun daina saka darussan da mutum ya fadi akan takardar sakamakon.

No comments:

Post a Comment