Saturday, 24 November 2018

Wani murgujejen dutse ya nufo Duniya: Zai iso gobe da tsakar rana

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Amurka, NASA ta fitar da gargadin cewa a gobe, Lahadi, 25 ga watan Nuwamba, wani murgujejen dutse zai wuce ta kusa da Duniyarnan tamu.


NASA tace wani tauraron tane ya hango wannan dutse da ya tinkaro Duniya kuma yake kan gudun wuce misali, a kiyasin NASA tace dutsen zai gitta ta kusa da Duniya da tazarar kilo mita miliyan 150.

Tace duk da a tunani da lissafin dan Adam wannan tazarace me nisa amma a lissafin sararin samaniya wannan gittawa tayi kusa kuma suna nan sun saka ido dan ganin yanda zata wakana, sun kara da cewa da misalin tsakiyar rana, bayan karfe 12:00pm ne ake tsammanin dutsen zai gitta.

A fasahar zamani ta kimiyya dai idan wani abu ya tunkaro Duniya wanda zai iyayin illa za'a iya hangoshi da kuma yi kiyasin irin illar da zai iyayi harma a dauki matakan rigakafi, saidai shi wannan dutse ba'a bayyana wata barazana da yake tafe da itaba.

A shekarar 2013 dai an taba samun wani abu da ya fashe a sama daidai kasar Rasha wanda yayi sanadiyyar fashewar gilasai har mutane kimanin 1000 suka jikkata, kamar yanda Express Uk ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment