Saturday, 17 November 2018

Wani shahararren mawakin kasar Ingila, Musulmi yayi Ridda

Tauraron mawakin kasar Ingila, Zayn Malik wanda ya taso cikin addinin Musulunci ya bayyana cewa yayi ridda, ya daina Sallah kuma be yadda ace sai an yi addu'a za'a yi yanka ba.


Zayn wanda mahaifanshi musulmai ne ya bayyanawa kafar British Vogue cewa, mahaifansu sun basu damar su zabi addinin da suke so, kuma shi ya taso ya karanci addinin musulunci kuma yana zuwa masallaci amma yana kara girma sai yaji addinin na fita daga ranshi.

Ya kara da cewa, da farko yayi shakkar fitowa ya bayyanawa Duniya amma yanzu yana ganin cewa kawai idan kai abin kirki abin kirki zai sameka.

Ya kara da cewa ya yadda akwai Allah amma be yadda akwai wuta ba.

Saidai Malik ya kara da cewa, yaji dadin tasowa cikin addinin musulunci kuma kowane addini yana nashi abubuwan masu amfani.

No comments:

Post a Comment