Friday, 30 November 2018

Wannan baiwar Allahn ta musulunta bayan bincike me zurfi tana neman gaskiya

Wannan wata baiwar Allah ce da ta samu shiriya ta karbi kalmar shahada bayan da ta jima tana bincike akan addinin musulunci da sauran addinai wannene na gaskiya.Ta bayyana cewa, ta lura littafin Baibul an cancanja shi sau da yawa kuma wasu ayoyin na karyata wasu amma Qurani ba zaka samu irin wadannan matsaloli a ciki ba.

Haka kuma tace tun tana cikin addinin kiristanci ta san cewa Annabi Isa ma'aikin Allahne.

Muna fatan Allah ya kara mata fahimtar addini ya kuma karo mana irinta.
No comments:

Post a Comment