Tuesday, 13 November 2018

Wutar daji mafi muni a tarihin Amurka ta tashi gari guda, mutane 42 sun mutu, 228 sun bace, 300,000 na gudun hijira

Wutar daji mafi muni a kasar Amurka wadda ta fara ranar Alhamis din makon jiya a jihar California ta yi sanadin mutuwar mutane 42, 228 sun bace, sama da 300,000 sun arce daga gidajensu.
Wutar dajin ta tashi wani gari guda da ake kira da Paradise inda rahotanni suka bayyana cewa kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na gine-ginen garin sun kone kurmus.


Wutar dajin tana watsuwa cikin gaggawa sanadiyyar iska me karfi dake kadawa kamar yanda masana suka bayyana ta jaridar Daily Mail Uk.


Shugaban kasar ta Amurka, Donald Trump a wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta ya dora alhakin watsuwar wutar cikin hanzari kan rashin kula da gandun daji yanda ya kamata, duk da makudan kudin da ake baiwa masu kula da dajin duk shekara, yayi barazanar tsayar da biyan kudin kula da gandun dajin muddin ba'a gyara ba.


Ya kuma yi kira ga mutane da su bi shawarar masu kokarin tserar da rayuwarsu dan tsira daga annobar wutar.


Mutane na ta guduwa suna barin gidajen su cikin motoci, a wasu lokutan ma idan suna tafiya cikin mota, saboda yawan matsi neman tsira akan samu cinkoso akan titi, dole suke sauka su taka a kafa dan kada wutar ta riskesu.


Motoci da gidaje da dama sun kone da kasuwanni da shaguna ciki hadda dabbobi.


Masu aikin ceto sun ta kokari, ana kashe wutar ana kuma ceton mutane haddama dabbobi.
Wannan wata magece da wutar ta kone ta kurmus.

Jiragen sama na kashe gobara nata shawagi suna zubawa wutar ruwa dan ta yi sauki.

Akwai gidajen manyan fitattaun mutane irin su, Kim Kardashian da mijinta Kanye West da Lady Gaga da Will Smith da abin ya shafa, dole suka fita suka bar gidajen nasu na alfarma dan tsira da rayukansu.


No comments:

Post a Comment