Wednesday, 7 November 2018

'Yan kasuwa sun yiwa El-Rufai ihu, sunyi watsi da tayin da ya yi musu

Wani abin mamaki ya faru a kasuwar Sheikh Abubakar Gumi da ke Kaduna inda 'yan kasuwar suka gwale gwamna Nasir El-Rufai na jihar bayan ya yi alakwarin sake gina musu shagunansu da gobara ta afkawa.


Rahottani sun bayyana cewar El-Rufai ya kai ziyarar bazata ne a kasuwar a ranar Talata bayan ya samu labarin cewar Sanata Shehu Sani mai wakiltan mazbar Kaduna ta Tsakiya ya ziyarci kasuwar a ranar Litinin.

An ruwaito cewar 'yan kasuwar sun katsewa gwamna El-Rufai hanzari yayin da ya ke jawabi inda suka rika kasa ihu suna cewa: "Bama so, Bama so, Shakaru hudu kawai za kayi."

Shehu Sani ya kai ziyara kasuwar ne a ranar Litinin misalin karfe 11 na safiya domin ganawa da mutanen yankinsa kuma sun karbe shi hannu biyu-biyu inda suka rika yabonsa kan yadda ya ke kusantar talakawa da kuma ayyukan da ya keyi a majalisa.

Sani ya bayar da gudunmawa na N1 miliyan ga wadanda gobara ta kone shagunansu da ke kusa da layin dogo a kasuwar kuma ya dauki alkawarin daukan nauyin karatun yaran 'yan kasuwan da suka rasu har na tsawon shekaru biyu.

A kwana-kwanan nan ne a Abuja, El-Rufai ya kallubalanci Sani da ya shiga cikin kasuwar ta Abubakar Gumi ya gani ko zai fito lafiya domin a cewar El-Rufai yan kasuwar suna fushi da shi sai dai Sani ya shiga kuma ya fita lafiya.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment