Wednesday, 28 November 2018

'Yan majalisar dattijai sun bukaci gwamnati data dakatar da karin haraji akan giya da taba

'Yan majalisar dattijai sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da karin kudin harajin da ta saka akan giya da taba dan tseratar da masana'antun dake yinsu a gida daga durkushewa.

'Yan majalisar sun bukaci dakatar da harajinne inda suka bukaci cewa a tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar tukunna kamin a zartar da wannan hukinci.

Tun a farkon shekarar nanne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dokar kara kudin haraji akan giya da taba.

No comments:

Post a Comment