Wednesday, 28 November 2018

'Yan sandan Dubai sun sayi motar aikin dansanda ta Daya a Duniya

 
Hukumar 'yansandan birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular Larabawa sun kaddamar da wata motar da suka bayyana ta a matsayin mafi afani a Duniyar aikin tsaro ta 'yansanda.An sakawa motar suna, Ghiath kuma kamfanin kera motoci na W motors na birnin na Dubaine suka kerata, motar na da kyamarori na musamman dake daukar hotunan fuskokin mutane da kuma lambobin motoci a shirin ko ta kwana ga masu aikata laifuka.

Dama dai hukumar 'yansandan ta Dubai na da manyan motocin alfarma masu gudu sosai da suke aiki da su sannan kwanakin baya suka bayyana cewa nan bada jimawa ba zasu kaddamar da mashin me tashi sama.
No comments:

Post a Comment